Amurka ta amince da siyar da makamai na dala biliyan 4.8 ga wasu kasashen Gabas ta Tsakiya

Amurka ta amince da siyar da makamai na dala biliyan 4.8 ga wasu kasashen Gabas ta Tsakiya

Kanfanin Tsaron Kasar Amurka ta sanar da cewa an amince da siyarwa kasashen Kuwait, Saudiyya da Misira makamai na dala biliyan 4 da miliyan 859 da dubu 500.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurkan ce ta amince da siyarwa Kuwait jiragen yaki masu saukar ungulu  da sauran kayayyakin tsaro na dala biliyan 4 da miliyan 400; haka kuma ta amince da siyarwa Saudiyya rokoki na dala miliyan 290 da kuma ma siyarwa Misira jiregen yaki na dala miliyan 169.9.

Wadannan amincewar siyar da makaman zasu tabbata ne idan har kwamitin tsaro a majalsar dattawan kasar Amurka bata ki amincewa dasu a cikin kwanaki 30 ba.


News Source:   ()