Amurka ta harba tauraron dan adam mai leken asiri samfurin "NROL-44" zuwa duniyar sama.
Labaran da aka fitar a shafin yanar gizo na "Space.com" na cewa, tauraron da zai yi aiyukansa a sirrance, an dauke shi da kumbon Delta-4 tare da harba shi ta tashar Cape Canaveral da ke jihar Florida.
Kamfanin United Launch Allience da hadin gwiwar Boeing da Lockheed Martin ne ya samar da tauraron.
Ba a bayyana wanne aiki tauraron dan adam din zai yi ba.
Sakamakon matsalolin da aka fuskanta a ranakun 26 ga Agusta da 26 ga Satumba ya sanya aka dage harba tauraron zuwa sama.