Amurka na shirin gindaya sharadin yin allurar riga-kafin Corona da 'yan kasar waje da ke son shiga kasar.
Labaran da Associate Press suka fitar na cewa, wani jami'in Fadar White House da ya nemi a boye sunansa ya bayyana cewa, gwamnatin Joe Biden ta dauki matakin farko na gindaya sharadin yin allurar riga-kafin Corona (Covid-19) ga dukkan 'yan kasashen waje da za su shiga kasar.
Dokar hana shiga Amurka ta tsawon kwanaki 14 na c, gaba da aiki ga wadanda ba 'yan kasa ba da suka je kasashen China, Schengen, Birtaniya, Ailan, Barazil, Afirka ta Kudu da Indiya.
haka zalika a yanzu ana neman shaidar ba a dauke da cutar Corona da aka karba a awanni 72 da suka gabata daga wajen dukkan fasinjojin da suka zo shiga Amurka.