Ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov ya tattauna da takwaransa na Amurka Mike Pompeo akan lamurkan Libiya, Siriya da Afghanistan.
Dangane ga sanarwar da ta fito daga ma'aikatar harkokin wajen Rasha, Lavro da Pompeo sun tattauna da juna.
Rasha da Amurka sun tattauna akan yadda za'a yi aiki tsakanin kasashen biyu domin samar da lumana a yankunan ta bin hanyar soja da kuma siyasa.
Haka kuma baya ga huldan kasashen biyu an kuma tabo lamurkan tsaron kasashen Libiya, Siriya da Afghanistan.