Amurka ba ta isa ta tirsasa mana ba - Ramaphosa

Amurka ba ta isa ta tirsasa mana ba - Ramaphosa

A jawabin da ya yi wa jama'ar ƙasar, Ramaphosa ya ce suna fuskantar ƙaruwar kishin ƙasa da kare muradunta da kuma mayar da hankali a kan takaitattun manufofi. 

Shugaban ya ce su a matsayinsu na mutanen Afirka ta Kudu ba za su bada-kai-bori-ya-hau ba a harkokinsu na cikin gida. Wadannan kalamai mayar da martani ne ga shugaba Trump wanda ya zargi gwamnatin Afirka ta Kudu da laifin kwace filayen Turai suna mallaka wa baƙaƙen fata, zargin da Ramaphosa ya yi watsi da shi. 

Elon Musk wanda haifaffen Afirka ta Kudu ne ke bai wa shugaba Trump shawara, kuma wannan na daga cikin dalilan da ya sa suka zargi ƙasar da nuna banbanci ga jinsin wasu mutane da kuma barazanar katse tallafin da Amurka ke bai wa ƙasar. 

Wata dokar da Ramaphosa ya rattaba wa hannu a makon jiya ta kunshi karɓe wasu filaye daga hannun jama'a idan buƙatar haka ta taso ba tare da biyan komai ba.

Mallakar fili a Afirka ta Kudu batu ne mai sarƙaƙiya sakamakon yadda Turawa ƴan kaɗan suka mamaye akasarin filayen noman kasar.

 A jiya Laraba, Sakataren Harkokin Waje, Marco Rubio ya sanar da cewar ba zai je kasar taron kasashen G20 da za'ayi a wannan watan ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)