Amnesty International: '' Yan sandan Ethiopia sun tsare 'yan Tigray ba bisa ka'ida ba'
Kungiyar Amnesty International ta zargi ‘yan sandan Ethiopia da kame wasu kabilu a yankin Tigray ba bisa ka’ida ba saboda asalinsu.
A cikin sanarwar da kungiyar ta fitar, an bayyana cewa an kame yan kabilar Tigray a Addis Ababa babban birnin kasar ba tare da izini ba bayan da kungiyar 'yan tawayen Tigray People Liberation Front (TPLF), wacce ta yi artabu da sojojin tarayya a arewa, suka kwace Mekelle, babban birnin jihar Tigray.
A cikin sanarwar, an lura cewa har yanzu ba a san inda daruruwan mutanen da aka kamen suke ba, kuma an jaddada cewa babu wani zargi da duniya ta sani akan wadannan mutanen da aka kame.
A cikin sanarwar, ‘yan jarida da ma’aikatan yada labarai su ma suna cikin wadanda aka tsare ba bisa ka'ida ba, kuma an bukaci gwamnatin Ethiopia da ta" kawo karshen kame-kame da ake yi ba bisa ka'ida ba ".
Kungiyar ta TPLF, wacce ta kwace mafi yawan babban birnin jihar, ciki har da Mekelle, ta sanar da cewa gwamnati ba za ta yi aiki da shawarar tsagaita wutar da ta ayyana ba.
Gwamnatin Ethiopia ta sanar a ranar 28 ga watan Yuni cewa ta ayyana tsagaita wuta a wani yanki a yankin Tigray, wanda ‘yan tawayen TPLF suka ce sun kame.