An sanar da cewa sanadiyyar ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a Kudancin Asiya wanda ya haifar da ambaliyar ruwa an rasa rayukan mutum 221.
Hukumomi sun bayyana cewa ambaliyar ruwan da ta janyo zaizayar kasa a garin Mumbai da ke kasar Indiya an samu gawarwaki 8 inda a fadin kasar mutum 101 suka rasa rayukansu. A Bangladesh kuwa mutum uku suka rasu.
Ambaliyar ruwa kuma yi sanadiyyar sanya miliyoyin mutane barin gidajensu a wasu yankunan kasashen Nepal, Bangladesh da Indiya.
Hukumomi a Indiya sun bayyana cewa lamarin ya shafi mutum miliyan 3.6 a fadin kasar inda kuma ya taba jihohi 33.
Ma'aikatar cikin gidan Nepal ta sanar da cewa daga ranar 12 ga watan Yuni ambaliyar ruwan ta yi sanadiyyar rasa rayukan mutum 117 a fadin kasar, inda kuma wasu 126 suka raunana, 47 kuma suka bata.
Bangladesh kuwa ta bayyana cewa a kasar mutum 3 sun rasu fiye da miliyan kuma sun kasance cikin mawuyacin hali sanadiyyar ambaliyar ruwa a kasar.