An sanar da cewa tsananin ruwan sama kamar da bakin kwarya ta yi sanadiyar hasara mai yawa a yankunan kasar lndonesiya da dama.
Hukumar bayar da agajin gaggawa a kasar ta bayyana cewa a yankin jihar Yammacin Java a yankin Sukabumi da kama Jakata an yi tsananin ruwan sama da ya haifar da ambaliyar ruwa.
A Sukabumi mutum 20 sun raunana inda kuma wasu 3 suka bata. An kuma samu hasarar dukiya inda fiye da gidaje 210 suka lalace.
Haka kuma wani gidan ibada ya tabu kuma wasu gadoji 10 sun lalace.