Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutane da dama a Indiya

Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutane da dama a Indiya

A Indiya, sakamakon fadowar tudun kankarar Nanda kan kogin Dhauliganga wanda ya janyo ambaliyar ruwa, mutane 14 sun rasa rayukansu.

Mahukunta sun bayyana cewa, gidaje da dama da cibiyoyin samar da makamashin 2 sun samu matsala sakamakon fadowar tudun kankarar Nanda kan kogin Dhauliganga na yankin Chamoli.

Bayan afkuwar ambaliyar ruwa, an sake ciro jikkunan mutane11 daga cikin ruwan wanda hakan ya kara adadin wadanda suka mutu zuwa 14, ana ci gaba da neman a kalla mutane 150 da suka bata.

'Yan sandan Chamoli sun bayyana cewar wadanda suka bata ma'aikatan cibiyoyin samar da lantarki ne, kuma an samu nasarar kubutar da mutane 15.

Rundunar Sojin Saman Indiya ta bayyana tana gudanar da aiyukan ceto ta sama.

'Yan sandan Iyakar Indiya-Tibet ma sun sanar da suna gudanar da aiyukan ceto a kusa da kauyen Raini da ibtila'in ya afku.


News Source:   ()