Ambaliyar ruwa da guguwar Ida ta janyo a arewa maso-gabashin Amurka ta yi sanadiyyar rasa rayuka 45.
Bayan jihar Lousiana da ke arewacin Amurka, guguwar Ida ta yi karfi a arewa maso-gabashin Amurka inda aka samu mamakon ruwan sama a jihohin New York, New Jersey, Pennsylvania, Maryland da Connecticut.
Mutane 13 sun mutu sakamakon ambaliyar ruwa a New York, A New jersy kuma adadin wadanda suka mutu ya karu zuwa mutane 23.
Tare da rasa rayukan da aka samu a Pennsylvania, Maryland da Connecticut, adadin wadanda suka mutu ya kai 45.
Gwamnan New Jersy Phil Murphy ya shaida cewa, ruwa ya mamaye ababan hawa da dama tare da tafiya da su.
Ana ci gaba da aiyukan ceto a yankunan da ambaliyar ruwan ta afku, ana kuma fargabar samun karin rasa rayuka.