Mutane 70 sun rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwan da mamakon ruwan sama ya janyo a jihar Pervan da ke Afganistan.
Kakakin Fadar Gwamnan Pervan Wahida Shahkar ya shaida cewar an samu ambaliyar ruwa a jihar sakamakon mamakon ruwan saman da aka fara a ranar Larabar nan a jihar.
Shahkar ya shaida cewar ya zuwa mutane 70 ne suka mutu yayinda wasu 100 suka samu raunuka sakamakon ibtila'in.
Ya ce gidaje da dama sun kasance a karkashin ruwa, kuma ana ci gaba da aiyukan kubutar da wadanda lamarin ya rutsa da su.