Mutane 174 ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwan da mamakon ruwan sama ya janyo a Yaman.
Bayanan da aka samu daga majiyoyin gwamnati sun ce sakamakon rashin kyawun yanayi a kasar mutane 40 sun mutu a yankunan da ke hannun gwamnati.
An bayyana cewar kaso 2 cikin 3 na wadanda suka mutu na garin Ma'arib na kudancin Yaman, kuma lamarin ya janyo jikkatar wasu mutanen da dama.
Sanarwar da mayakan Houthi suka suka fitar ta ce mutane 134 ne suka mutu inda wasu 124 suka jikkata sakamakon ambaliyar ruwa a San'a Babban Birnin Yaman.