Bayanan farko sun bayyana cewa, a kalla mutane 10 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku a yankunan Iran daban-daban.
Shugaban Kungiyar Bayar da Agajin Gaggawa, Taimako da Kubutar da Jama'a ta Iran Mahdi Velipur ya zanta da Kamfanin Dillancin Labarai na Ma'aikatan Iran (ILNA) game da ambaliyar ruwan da ta afku a yankunan arewa maso-gabas, tsakiya da kudu maso-gabashin kasar.
Velipur ya ce, "Sakamakon mamakon ruwan sama an samu ambaliyar ruwa a jihohin Isfahan, Yezd, Horasan ta Kudu, Horasan-i Rezevi, Kirman, Simnan, Tahran da Sistan-Belujistan. A jihohin Yezd, Horasan ta Kudu da Kirman an gano jikkunan mutane 10 da suka bata. Ana ci gaba da neman wani mutum 1."
Velipur ya kara da cewa, kauyuka 47 a gundumomi 6 ibtila'in ambaliyar ruwan ya shafa, kuma daruruwan mutane na bayar da taimako a aiyukan ceto da ake yi.