An sanar da cewa ambaliyar ruwar da ta afku sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a jahohin Sabah da Sarawak dake kasar Malaysia ta yi sanadirar kauran fiye da mutum dubu biyar daga matsugunansu.
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Sabah ce ta sanar da cewa sanadiyar ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi ta kwanaki uku al'umman yankin da aka kwashe sun kai dubu 4 da 772.
Hukumar ta Sarawak ta bayyana cewa an kwashe fiye da mutane 326 zuwa yankin da lamarin bai shafa ba.
Jami’an sun bayyana cewa za a ci gaba da ruwan sama, sabili da haka jami’ai sun ce za a kara yawan wuraren tsaro a jihohin biyu.