Kasar China ta sanar da cewa daga farkon shekarar bana kawo yanzu annobar kwararar ruwa kawo yanzu ta yi sanadiyar rayuka 121.
A jaridar People's Daily ta Komunist an bayyana cewa hukumar bayar da agajin gaggawan kasar ta sanar da cewa daga watan Janairu kawo yanzu a yankuna 26 kwararar ruwa ta shafi fiye da mutum miliyan 19.
Sanarwar ta kara da cewa gonarnakin da girmansu ya kai hekta miliyan daya da rabi kuma sun tabu lamarin da ya haifar da hasarar biliyan 5.8.