Dubban mutanen da gidajensu suka ruguje sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya a Koriya ta Arewa an kwashe su.
Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya mamaye daruruwan kadadan gonaki kuma ya lalata gadoji da dama.
A cikin labaran gidan talabijin Koriya ta Arewa, an sanar da cewa ruwan sama mai karfin gaske da ya yi tasiri a yankin arewa maso gabashin kasar ya lalata gidaje 1,170, ya bar su a karkashin ruwa kuma mutane dubu 5 da ke zaune a cikin gidajen dole ne a kwashe su zuwa wuraren da zasu fake.
An bayyana cewa ruwan sama kamar da bakin kwarya a lardin Hamyong ta Kudu ya mamaye daruruwan hekta na filayen noma tare da lalata gadoji da dama.
An yi hasashen cewa za'a ci gaba da yin ruwan sama mai yawa a yankin har na tsawon kwanaki.