A arewacin jihar Sulawesi ta kasar Indonesiya, mutum 1 ya mutu sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku, yayin da ta sahfi mutane sama da dubu 22.
Raditya Jati, Shugaban Cibiyar Ba da Labarai da Sadarwa na Hukumar Bayar da Agaji ta Kasa ya bayyana cewar an samu ruwan sama mai karfi a yankin na Kudancin Bolaang Mongondow da ya haddasa ambaliyar a wurare 7.
Ya kara da cewa mutane dubu 22 da 655 ne ambaliyar ta shafa kuma mutum 1 ne ya mutu a bala'in ambaliyar ya zuwa yanzu.
Jati ya ba da sanarwa cewa gidaje 64, gadoji 5 da kuma wasu hanyoyi sun lalace sakamakon ambaliyar ruwan a yankin.