Mutane 4 da suka hada da yara kanana 2 sun rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwan da mamakon ruwan sama ya janyo a jihar Hayber Pahtunhva da ke Pakistan.
Sanarwar da aka fitar daga Hukumar Yaki da Annoba da Ibtila'i ta jihar Hayber Pahtunhva ta ce, mamakon ruwan sama a yankunan Karak da Upper Dir ya janyo ambaliya.
Sakamakon ambaliyar da mamakon ruwan sama ya janyo a Karak da Upper Dir mutane 4 da suka hada da yara kanana 2 sun mutu. Wasu mutanen 3 kuma sun jikkata.
Labaran da jaridun yankunan suka fitar sun ce, gidaje da dama sun samu matsala inda ruwa ya mamaye gonaki.
Haka zalika an dakatar da zirga-zirgar ababan hawa a garuruwan Gangdhal da Sheringal, a yankin Swat kuma ruwa ya mamaye gidaje da wuraren sana'a da dama.