Mutane 24 sun rasa rayukansu, wasu 18 sun jikkata sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku a arewa maso-gabashin Pakistan.
Jami'in yankin Pencap Muhammad Asghar ya shaida cewar gidaje da dama sun rushe samakkon ambaliyar da mamakon ruwan sama ya janyo.
Mutane 24 sun rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwan, wasu 18 sun samu raunuka, kuma an samu mafi yawan rasa rayukan a gidajen da suka rushe.
A tsakanin watannin Yuni da Satumba ana samu mamakon ruwan sama a yankunan kudancin nahiyar Asiya, inda a kowacce shekara ake samun ibtila'in ambaliya.