An kwashe daruruwan mutane daga gidajensu sakamakon ambaliyar ruwa da mamakon ruwan sama ya janyo a yankin Canterbury na kasar Niyuzelan.
A wasu yankunan ruwan ya kai zurfin santimita 40 wanda hakan ya sanya aka aiyana dokar ta baci a kasar.
A aiyukan ceto da sojoji suka taimaka wajen gudanarwa, an kubutar da sama da mutane 50 ta hanyar amfani da jirgin sama mai saukar ungulu.
Firaministar Niyuzelan Jacinda Ardern ta bayyana za ta ziyarci garin Christchurch don ganewa idanuwanta.