Mutane 45 sun rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwan da ta afku a Kolombiya bayan samun mamakon ruwan sama.
Labaran da jaridun kasar suka fitar sun rawaito Hukumar Bayar da Agaji da Magance Ibtila'o'i (UNGRD) na cewa, tun lokacin da aka fara ruwan sama kogunan kasar su ke cika kuma ake samun zaftarewar kasa.
An bayyana mutuwar mutane 45 a ambaliyar da ta shafi kusan dukkan yankunan Kolombiya, haka zalika wasu mutanen 23 sun jikkata yayinda wasu 3 kuma suka bata.
Ambaliyar ruwa da ballewar kogunan ta illata iyalai dubu 3,451, an kuma kwashe mutane dubu 36 daga matsugunansu.
Manyan jihohin Antioquia, Valle del Cauca, Narino, Huila da Cundinamarca ne ambaliyar ruwan ta fi shafa.
Mahukunta sun yi kira ga jama'a da su nisanci gabar koguna, gulabe da hanyoyin a wannan lokaci na damuna da aka shiga.