A lardin Kalimantan da ke Kudancin Indonesiya, adadin wadanda suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku bayan mamakon ruwan saman da ya fara tun daga ranar 12 ga Janairu ya karu zuwa 21.
Firmansyah, jami’in soja na Kudancin Kalimantan ya bayyana cewar mutane dubu 63 da 608 ne suka rasa matsugunansu sakamakon ambaliyar a wurare daban-daban 11 da suka hada yanki da birane.
Firmansyah ya ce ya zuwa yanzu mutane 21 ne suka rasa rayukansu a yankin da ambaliyar ta shafi gidaje dubu 66 da 763 da mutane 342 dubu 987.
Da yake bayyana cewar gadoji 21, wuraren ibada 110 da makarantu 76 ambaliyar ta lalata a duk fadin jihar, Firmansyah ya ba da rahoton cewa ambaliyar ta kuma lalata kadada dubu 18 na filin kasar noma.