A kalla mutane 12 ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku bayan samun mamakon ruwan sama a jihar Henan da ke tsakiyar China.
Kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya shaida cewa, bayan samun ruwan sama kamar da bakin kwarya a garin Zhengzhou an ambaliya ta afku tare da janyo asarar rayuka.
Ya zuwa yanzu ma'aikatan ceto sun ciro jikkunan mutane 12 sannan an kwashe mutane sama da dubu dari zuwa wasu yankunan.
Sanarwar da gwamnatin yankin Zhengzhou ta fitar ta bayyana ibtila'in a matsayin mai girma.
Tun ranar 17 ga Yuli ake tafka ruwan sama a jihar Henan.
Ruwa ya mamaye fasinjoji a cikin jiragen kasa na karkashin kasa a garin Zhengzhou babban birnin jihar ta Henan.