Ambaliya tare da zaftarewar kasa a Indonesiya

Ambaliya tare da zaftarewar kasa a Indonesiya

Mutane 3 sun rasa rayukansu, wasu 9 sun mata sakamakon ambaliya da zaftarewar kasar da mamakon ruwan sama ya janyo a jihar Sumatra ta Arewa dake Indonesiya.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa ta shaida cewa, bayan zaftarewar kasar da ta afku a garin Marancar mai cibiyar samar da makamashin lantarki, kasa ta danne mutane 12 wadanda aka iya ciro jikkunan 3 daga ciki.

Sanarwar ta ce ana ci gaba kokarin neman sauran mutane 9 da ke karkashin kasar.

 


News Source:   ()