Mutane 40 sun rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwan da ta afku a jihar Nuristan ta gabashin Afganistan da ke iyaka da Pakistan.
Shugaban Majalisar Shura ta Jiha Sadullah Payandazoi ya shaida cewa, bayan mamakon ruwan sama da aka samu a gundumar Kamdish ta Nuristan ambaliyar ruwa ta barke.
Payandazoi ya shaida cewa, mutane 40 sun mutu sakamakon ambaliyar ruwan,kusan gidaje 80 kuma sun kasance mamaye da ruwa, kuma har yanzu ba a da labarin wasu mutanen da dama.
Ya bayyana ana ci gaba da aiyukan ceto, kuma har yanzu ba a samu damar kai kayan agaji ba a yankin da Taliban ta ke da karfin iko.