Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ɗimbim jama’a su ka fito wani dandali a tsakiyar babban birnin ƙasar don ruguntsimin samun ƴanci.
A jiya Litinin ne jam’in sa kai na Syria, wato Syrian White Helmets su ka ce su na neman wasu ƙofofin sirri ko kuma maɓuyar ƙarƙashin ƙasa na gidan yarin Saydnaya don gano waɗanda ke garƙame, kuma su ka maƙale.
Assad ya tsere daga Syria a yayin da ƴan tawaye su ka kutsa babban birnin ƙasar, lamarin da ya kawo ƙarshen shekaru 50 na mulkin iyalan Assad a ƙasar, da ta sha fama da yaƙi mafi muni a cikin wannan ƙarni.
Daga cikin ƙadarorin da hamɓararren shugaban ya gada a gun mahaifinsa, Hafez al-Assad har da ruƙunin gidajen yari mai ƙunshe da cibiyoyin tsare mutane, waɗanda ake amfani da su wajen ladafta masu banbancin ra’ayi ko kuma waɗanda ake zargi da i wa jam’iyyar Baath karan tsaye.
A yayin hare-haren da ƴan tawayen su kaƙaddamar a ranar 27 ga watan Nuwamba, mayaƙan sun karbe biranen da ke ƙarƙashin jagorancin Al-Assad, da buɗe gidajen yari don sakin dubban fursunoni.
A yayin da Syria ta shafe shekaru 13 tana yaƙi, cikin ƴan kwanaki kaɗan ne kawai aka kifar da gwamnatin ƙasar, da ƴan tawaye ƙarƙashin jagorancin Hayat Tahrir Al-Sham suka yi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI