Yayin bikin Mauludin dai bisa al’ada Musulmin galibi mabiya Sufaye kan yi dafifi tare da yawaita zikiri salatin Annabi baya ga mabanbantan kasidun yabo ga fiyayyen halitta, inda a bangare guda Iyaye kan yiwa yaransu sabbin dinkuna yayinda mawadata kan yanka raguna da shanu baya ga girke-girken alfarma don hidimar ranar da ake yiwa gagarumin biki.
Kusan dukkanin kasashen Duniya da Musulmi ke da rinjaye na gudanar da bukukuwan na Mawludi tare da bayar da hutun ranar a kowacce shekara don gudanar da shagulgula in banda kasashen Saudiya da Qatar wadanda ke kallon bikin a matsayin lamarin da ba karbabbe ba a addinin Islama.
To domin sanin muhimmancin wannan rana ga Musulmi? Ku latsa alamar sauti donjin tattaunawar da Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya yi da Sheikh Mansur Ibrahim da ke garin Kaduna a Najeriya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI