Daraktan Sadarwar a fadar shugaban kasar Turkiyya Fahrettin Altun ya tattauna da jakadan China a Ankara Liu Shaobin.
Altun ya yada a shafinsa na Twitter inda yake cewa,
"Mun tattauna da jakadan China a Ankara Liu Shaobin. Shugaba Erdogan ya mika sakon gaisuwa ga takwaransa na China ga Shaobin. An tattauna akan allurar riga-kafin Covid-19 da kuma lamurran tsakanin kasashen biyu"