An sanar da cewa wani Bahafasdine dake tsare a wani gidan yârin Isra’ila ya mutu bayan an yi masa allurar rika-kafin Korona.
Hukumar gidan yârin ce ta sanar da cewa Maher Deeb Saasa mai shekaru 45 daga Qalgilah a Arewacin Gaza wanda ya yi fama da rashin lafiya ya rigamu gidan gaskiya.
Iyalan mamacin mai ‘ya’ya shida sun bayyana cewa an yi rikon sakainar kashi game da rashin lafiyarsa a shekaru 15 da ya kwashe a gidan yâri.
Iyalan nasu sun bayyana cewa sun shirya kasidar da zasu aikawa hukumar kare hakkin bil adama domin bi musu hakkinsu akan rashin rayuwar dan uwannasu da suke zargin sakaci akan kula da lafiyarsa ya haifar da hakan.
Isra’ila dai ta yanke hukuncin yiwa ‘yan fursuna allurar riga-kafin Korona duk da dai cutar na ci gaba da yaduwa a gidajen wakafin.