Kamfanin kera magunguna na Amurka, Moderna ya ba da sanarwar cewa allurar riga-kafin sabon nau'in kwayar cutar corona (Covid-19) da ta samar tana ba da kariyar kashi 93 cikin ɗari watanni 6 bayan yin kashi biyu na allurar.
Babban jami’in Moderna, Stephane Bancel a cikin wata sanarwa ya ce,
"Mun yi farin ciki cewa allurar riga-kafinmu ta Covid-19 ta nuna inganci mai ɗorewa. Duk da haka, muna sane da cewa nau’in Delta babban barazana ne. Don haka dole ne mu yi taka tsantsan."
Bancel ya bayyana cewa allurar Covid-19 din da suka samar har yanzu tana ba da kariyar kashi 93 cikin ɗari watanni 6 bayan yin allurar.
Kamfanin samar da allurar riga-kafin, Pfizer-BioNTech, ya yi irin wannan sanarwar a makon da ya gabata, inda ya ba da rahoton cewa allurar riga-kafin da ya samar yana ba da kariyar kashi 91 cikin dari watanni 6 bayan yin kashi biyu na allurar.