Allurar riga-kafin Corona ta Pfizer/BioNTech na aiki a kan yara kanana

Allurar riga-kafin Corona ta Pfizer/BioNTech na aiki a kan yara kanana

An bayyana cewa, allurar riga-kafin Corona (Covid-19) da kamfanin Amurka na Pfizer da na BioNTech da ke Jamus suka samar na aiki 100 bisa 100 a kan yara masu shekaru 12 zuwa 15.

Pfizer da BioNTech sun sanar da gwada allurar riga-kafin a kan yara kanana 'yan shekaru 12 zuwa 15 su dubu 2,260.

Sanarwar da suka fitar ta ce, an gano yadda allurar ta ke kara karfafa garkuwa da ke jikin yara, kuma ta ma fi karfin aiki a jikinsu sama da jikin manyan mutane. 

A gefe guda, ba a samu wani da aka yi wa allurar ya kamu da cutar ba, amma kuma an samu wasu 18 da aka yi wa allurar karya sun kamu da ita.

Haka zalika an bayyana cewa, an samu yaran da irin alamun zazzabi, gajiya, ciwo da karkarwa da aka gani a tare da manya bayan yi allurar musamman bayan karbar ta biyu.

BioNTech na shirin mika bukatar amincewa da yin allurar ga 'yan shekaru 12 zuwa sama a Amurka da kasashen Turai.

Kamfanin na ci gaba da gwajin allurar a kan yara masu shekaru 6 zuwa 11.


News Source:   ()