Alluran riga-kafin Covid-19 na farko sun isa Libiya

Alluran riga-kafin Covid-19 na farko sun isa Libiya

Libiya ta sami jigilar farko na alluran riga-kafin Covid-19 101,250 da Kamfanin Sputnik-V na Rasha ya samar.

A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Lafiya ta Libiya ta fitar, an bayyana cewa allurai dubu 101 da 250 da Kamfanin Sputnik-V na Rasha ya samar sun isa Tripoli tare da kokarin Firaministan Libiya, Abdulhamid Dbeibah.

A cikin sanarwar an bayyana cewa za a adana alluran a wuraren ajiyar kaya na Ma'aikatar. Ba a bayar da wani bayani game da lokacin da za a fara yi wa mutane alluran ba.

Firaminista Dbeibah ya ce “Mun sami damar isar da alluran riga-kafin Covid-19 na farko, ragowar za su zo a jere" 

Dbeibah ya bukaci 'yan kasar Libiya da su yi rajistar karbar allurar riga-kafin Covid-19 a tsarin da Cibiyar Yaki da Cututtuka ta kasar Libiya ta kirkiro a watan jiya.


News Source:   ()