A kasar Girka an gudanar da zanga-zangar kalubalantar yunkurin tsunke bakin aljihu da gwamnatin kasar ke da niyyar yi.
A babban birnin Atina dinbin masu zanga-zangar sun karba kirar Jam'iyyar Komunist inda suka taru a filin shakatawar Omonia. Masu zanga-zangar tare da rere taken "Ba'a bukatar 'yan sandan gwamnati" sun yi tattaki har zuwa filin Sintagma.
Zanga-zangar da aka gudanar domin kalubalntar manufofin matsin lamban gwamnati ya yi tasiri a wasu biranen kasar da dama.
A ranar 29 ga watan Yuni aka mika doka da zata sanya yankewa wadanda suka gudanar da munanan zanga-zanga har tsawon shekaru biyu a gidan yari.