Al'umman kasar Kanada na ganin cewa ya kamata a gurfanar da Isra'ila a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya saboda laifukan yaƙi da ta aikata.
Sakamakon binciken jin ra'ayin jama'a da kungiyoyi masu zaman kansu har guda 3 suka gudanar mai taken EKOS Research, da suka yada da sunan "Babu nuna banbanci: Al'umman Kanada na Bukatar a kalubalanci Isra'ila" ya nuna cewa,
Kashi 84 cikin darin wadanda suka bayar da amsa a binciken jin ra'ayin jama'an na ganin ya kamata a gurfanar da Isra'ila a Koton Hukunta Manyan Laifuka domin ta aikata laifukan yaki.
Rahaton ya bayyana cewa kaso 86 cikin darin al'umman Kanada na kalubalantar kasarsu akan yadda ta sanya ido akan take hakkokin bil adama da Isra'ila ke yi don tana abokiyar huldan kasar.