'Yan kasar Azabaijan dubu 2,823 ne suka yi Shahada a lokacin da kasar ke gwagwarmayar kwato yankunanta da Armeniya ta mamaya a Karabakh.
Ma'aikatar Tsaro ta Azabaijan ta sanar da cewa, daga ranar 27 ga Satumba zuwa 10 ga Disamba da Armeniya ta amince an cinye ta da yaki tare da sanya hannu, 'yan Azabaijan dubu 2,823 ne suka yi Shahada a Karabakh.
A ranar 27 ga Satumban 2019 ne Azabaijan ta fara kai farmakai inda ta kwace manyan garuruwa 5, kanana 4 da kauyuka 286. 'Yan mamaya sun kuma janye daga lardunan Agdam, Lacin da Kelbejer.