Akidar nuna kyamar Musulmai a cikin al'ummomin kasashen Yamma ya kai matakin da bai kamata a sanyawa ido ba.
Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Yavuz Selim Kiran ya bayyana hakan, yana mai jaddada cewa wata barazana ce da ke ci gaba a tsari da yanayin siyasa a Turai ke kokarin mayar da nuna kyamar Musulunci da wariyar launin fata ba komai ba.
Kwamitin kula da karuwar nuna wariyar launin fata da kyamar addinin Islama a Turai, wanda aka kafa a karkashin Kwamitin Kare Hakkin Dan-Adam na Majalisar Dokokin Turkiyya, ya yi wata zama na musanman a karkashin jagorancin shugaban jam'iyyar adalci da ci gaba ta kasar Turkiyya Hakan da Cavusoglu.
Da yake jawabi a wurin taron, Kiran ya jaddada kokarin da ake yi na halalta ayyukan kyamar Musulunci bisa dalilai na doka a Turai kuma ya ce babban kuskure ne a yi ta'alaka ko gabatar da hare-haren nuna wariyar launin fata, kyamar baki da Musulmi a matsayin ayyukan mutum daya.
Bai kamata a sanya ido ga irin matsalar nuna wariya ta ko wace fanni dake karuwa a Turai ba.
Da yake ba da misalai na ayyukan nuna kyamar Musulmai da kyamar baki da hare-hare a kasashen Yammacin Turai, ciki har da Faransa, Jamus, Austria da Denmark, Kiran ya nuna gaskiyar cewa wadannan hare-haren na da matukar illa ga rayuwar al'umar Turkawa da Musulmai da ma ga harkokin siyasa, tattalin arziki da zamantakewasu na yau da kullun.