Afrika na buƙatar aƙalla dala triliyan 1.3 kowacce shekara don magance dumamar yanayi

Afrika na buƙatar aƙalla dala triliyan 1.3 kowacce shekara don magance dumamar yanayi

A wajen taron sauyin yanayi na birnin Baku da ke gudana yanzu haka, cikin murya ɗaya ƙasashen Afrikan sun buƙaci kuɗaɗe har dala triliyan 1.3 kowacce shekara don yaƙi da dumamar yanayin, da kuma samar da makamshin da baya gurbata muhalli a ƙasashensu.

Cikin ƙudin kuma, ƙasashen Afrika na fatan ganin an shawo kan annoba da kan faru da suka haɗar da ambaliyar ruwa, fari da kuma kwararar hamada wadda ke da alaka da sauyin yanayi.

Da yake ƙarin haske Seyni Nafo mai magana da yawun ƙungiyar ƙasashen Afrika da suka halarci taron ya ce a  shekarar 2025 da ke tafe, Afrika na buƙatar tallafin gaggawa na dala biliyan 105 zuwa 115 don yaki da matsalar.

Mr Seyni ya ce daga 2025 zuwa 2030 kuma Afrika na buƙatar aƙalla dala triliyan 1.22 kowacce shekara saboda shawo kan matsalar.

Shima a nasa ɓangaren wakilin jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo a wajen taron Tosi Mpanu Mpanu cewa yayi babbar buƙatar Afrika a yanzu itace taƙaita ragaitar gurɓatacciyar iska, ta hanyar samar da makamashi mara gurɓata muhalli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)