Girgizar kasa mai karfin awo 7.3 ta afku a lardin Qinghai na kasar China.
Bayan girgizar kasa mai karfin awo 6.1 da ta afku a birnin Dali da ke arewa maso yammacin kasar, an sake samun wata girgizar kasa mai karfin awo 7.3 a jihar Qinghai.
Hukumar Kula da Yanayin Kasa ta Amurka (USGS) ta sanar da cewa gurin da girgizar kasa ta fi afkuwa ita ce gundumar Madoi.
Yayinda da mahukuntar gundumar basu sanar da ko girgizar kasar, wacce ta afku a zurfin kilomita 10 a karkashin kasa ta janyo asarar rai ko raunuka ba, an ba da rahoton cewa wasu gine-gine sun lalace.
A girgizar kasar ta farko, mutum daya ya mutu kuma mutane 6 sun samu raunuka.