Mataimakin shugaban kasar Afghanistan Server Danış ya bayyana cewa lokaci ya yi da ya kamata kungiyar Taliban ta zauna a kan teburin sulhu.
Danış, a wani biki da aka gudanar a babban birnin kasar Kabul ya yi bayani akan matakan samar da zaman lafiya a kasar ta Afghanistan.
Ya bayyana cewa gwamnatin Afghanistan ta kauda dukkan kalubalolin da za su hana zaman sulhu tsakaninta da sauran kungiyoyi, a halin yanzu kungiyar Taliban ce ta rage.
Ya kara da cewa a halin yanzu ya kamata kungiyar Taliban ta amince da zama a kan teburin sulhu da gwamnatin kasar.
Kasancewar yadda gwamnatin Afghanistan ta kammala musayar fursunoni tsakanin ta da kungiyar Taliban ake ganin nan bada jimawa ba Taliban za ta fara zaman sulhu da gwamnatin kasar.