Afghanistan ta zargi Pakistan da kai mata hari

Afghanistan ta zargi Pakistan da kai mata hari

An yi ikirarin cewa a harin da aka kai da roka a jihar Kandahar dake kudancin Afghanistan mai iyaka da kasar Pakistan farar hula 15 sun rasa rayukansu.

Mai magana da yawun walin Kandahar Bahir Ahmadi, ya shaidawa manema labarai da cewa dakarun Pakistan sun kai hari da roka a garin Spin Buldak dake jihar Kandahar mai iyaka da kasar Pakistan.

Ahmadi, ya kara da cewa a harin farar hula 15 sun rasa rayukansu inda kuma wasu 80 suka jikkata.

Ma'aikatar harkokin tsaron kasar Afghanistan ta fitar da sanarwar cewa dakarun Afghanisatn dake kan iyakar Pakistan sun shirya tsaf domin mayar da martani kuma an basu izinin yin hakan.

 


News Source:   ()