Afghanistan ta haramtawa kafofin yada labarai wallafa hotunan halittu masu rai

Afghanistan ta haramtawa kafofin yada labarai wallafa hotunan halittu masu rai

Kakakin ma’aikatar yaƙi da munanan ɗabi’un ta Afghanistan Saiful Islam Khyber ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa, za a aiwatar da wannan dokar ce ta hanyar bayar da shawara, nasiha, har da lallami, saɓananin yin amfani da ƙarfi.

Khyber ya ce tuni aka fara ƙoƙarin aiwatar da dokar a garin Kandahar da kuma arewacin Takhar, yunkurin da ke tafe a sauran larduna.

Baya ga hana kafofin yaɗa labarai wallafa hotunan hallitu masu rai, ƙunshin sabuwar dokar gwamnatin ta Taliban za ta haramta izgilanci da yin wasa ga Addinin Islama. Sai kuma hana jama’ar gari amfani da wayoyin hannu da sauran na’urori wajen ɗaukar hotunan hallitun masu rai, da kuma kallonsu.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da gwamnatin Taliban ke ɗaukar irin wannan mataki a Afghanistan ba, domin yayin wanzuwar gwamnatinta daga shekarar 1996 zuwa 2001, kafafen yaɗa labarai musamman gidajen Talabiji ba sa nuna hotunan halittu masu rai.

Bayanai sun ce bayan sake karbar jagorancin ƙasar ta Afghanistan a shekarar 2021, gwamnatin Taliban ta bayar da  umarnin daina nuna fuskokin mata da maza yayin nuna tallace-tallace, sai kuma rufe idanun hotunan kifayen da ake wallafa wa a takardun gidajen abinci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)