Afganistan ta janye jami'an diplomasiyyarta daga Islamabad Babban Birnin Pakistan sakamakon garkuwa da 'yar jakadanta da aka yi.
Ma'aikatar Harkokin Wajen Afganistan ta sanar da cewa, an dauki wannan mataki ne bayan an yi garkuwa da 'yar jakadansu a Islamabad Najibullah Alikil.
Sanarwar ta ce, Afganistan ta janye jami'anta har nan da lokacin da za a kamo tare da hukunta masu garkuwar sannan a dauki kwararan matakan tsaro da suka dace.
Ma'aikatar Harkokin Wajen Pakistan ta bayyana matakin na Afganistan a matsayin abun takaici.
Wasu da ba a san ko su waye ba ne suka yi garkuwa da 'yar jakadan Afganistan a Islamabad Silsila Aliki mai shekaru 26 inda bayan zaluntar ta da suka yi suka sake ta.