Adadin wadanda suka rasa rayukansu a harin ta'addanci a Burkina Faso ya haura 160

Adadin wadanda suka rasa rayukansu a harin ta'addanci a Burkina Faso ya haura 160

Adadin wadanda suka rasa rayukansu a wani harin ta'addanci da aka kai a wani kauye da ke arewacin Burkina Faso ya kai 160.

A cewar bayanan da aka karbo daga majiyoyin tsaro, ana fargabar cewa adadin wadanda suka mutu zai karu fiye da yadda aka bayyana, saboda yawan wadanda suka ji munanan raunuka a harin ta’addancin da aka kai a kauyen Yaghga da ke yankin Sahel a daren da ya hada Juma’a zuwa Asabar.

A kasar, inda aka ayyana zaman makoki na kwana uku daga ranar Asabar, kungiyoyin kasa da kasa da dama sun la'anci harin.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi Allah wadai da wannan harin wanda ya bayyana a matsayin "abin kyama", sannan ya yi kira ga kasashen duniya da su kara bayar da goyon bayansu ga kasashen da ke yaki da ta'addanci.

A cikin bayanin da Tarayyar Turai ta yi, an bayyana cewa, wannan harin na "dabbanci" an yi Allah wadai da shi, ta kuma sake maimaita goyon bayanta ga yaki da ta'addanci a Burkina Faso.

Shugaban kasar Ivory Coast Alassane Ouattara shi ma ya yi Allah wadai da harin tare da bayar da sakon hadin kai ga mutanen Burkina Faso.

Ita ma Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta yi bayani tare da yin Allah wadai da harin.


News Source:   ()