Adadin wadanda suka kamu da Korona a gasar Olympic Tokyo ya haura 220

Adadin wadanda suka kamu da Korona a gasar Olympic Tokyo ya haura 220

Jimlar mutane 220 da aka amince da su don wasannin Olympics na Tokyo 2020 sun kamu da cutar Korona.

Kwamitin kungiyar ta tabbatar da cewa karin mutane 27, ciki har da 'yan wasa uku, sun kamu da COVID-19, wanda ya kawo adadin wadanda aka samu dauke da cutar a wasannin zuwa 220.

Sabbin mutanen da suka kamu da cutar sun killace kansu.

Gasar da aka dage daga shekarar 2020 zuwa bana sabili da bulluwar kwayar cutar Korona, an yi tunanin za'a samu 'yan kallo da dama amma saboda sabuwar nau'in cutar wuraren wasanni sun kasansce fili fallau.


News Source:   ()