A Amurka, adadin wadanda suka yarda da aiyukan Shugaba Joe Biden ya ragu zuwa kashi 50 cikin dari.
Wani binciken jin ra’ayin jama’a da aka gudanar ya nuna cewa kashi 90 na ‘yan Democrat, kashi 12 na ‘yan Republican da kashi 48 cikin 100 na masu zaman kansu sun amince da cewa shugaba Biden ya gudanar da aiyukan sa yadda ya kamata.
Binciken ya nuna cewa kimar Biden a tsakanin ‘yan Democrat da masu cin gashin kansu ya yi kasa a karon farko tun lokacin da ya shigo Fadar White House, inda gaba daya matsakaicin ya fadi zuwa kashi 50 cikin 100 a wannan watan daga kashi 56 cikin dari a watan Yuni.
Masana da suka kimanta sakamakon binciken da aka gudanar tsakanin 6 da 12 ga watan Yuli, sun danganta raguwar yarda da Biden ga hauhawar farashi ga masu siyan kaya duk da wasu ci gaba masu kyau da aka samu na tattalin arziki, raguwar allurar riga-kafi da karuwar mutanen da ke kamuwa da sabon nau'in kwayar cutar corona (Covid-19) a cikin makonnin da suka gabata.