Ya zuwa lokacin nadar wannan rahoto bayanai sun ce gobarar dajin da ke ci gaba da tafka ɓarna a birnin na Los Angeles ta raba mutane kusan dubu 200,000 da muhallansu bayan ƙone faɗin kasar da ya zarce kadada dubu 30, yayin da gine-gine fiye da dubu 10 suka salwanta.
Tun a jiya Alhamis mahukunta suka kiyasta cewar girman hasarar da aka tafka sakamakon wannan ibtila’i ya zarta dalar Amurka biliyan 50.
Jami’an kashe gobara kusan dubu 1 da 500 tare da taimakon jiragen sama ke fafutukar ganin sun kawo ƙarshen wutar dajin amma lamarin ya ci tura sakamakon iska mai karfin gudun kilomita aƙalla 160 a sa’a ɗaya da ke daɗa rura wutar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI