Adadin mutanen da suka yi shahada a haren-hare da Isra'ila ta kai Gaza

Adadin mutanen da suka yi shahada a haren-hare da Isra'ila ta kai Gaza

Wani Bafalasdine da Isra'ila ta jikkata a hare-haren kwanaki 11 da ta fara kaiwa Zirin Gaza a ranar 10 ga watan Mayu ya yi shahada, yayinda jimillar mutanen da suka rasa rayukansu a hare-haren na Isra'ila ya tashi zuwa mutane 254.

A wata rubutacciyar sanarwa da Ma'aikatar Lafiya ta Falasdin a Gaza ta fitar, an bayyana cewa wani Bafalasdine da ya jikkata a hare-haren Isra'ila ya yi shahada.

Rubutacciyar sanarwar da Ma'aikatar Lafiyar ta Falasdin da ke Zirin Gaza ta fitar ta bayyana cewa, tare da karin mutumin, jimillar mutanen da Isra'ila ta kashe a hare-haren da ta kai ya tashi zuwa mutane 254. Shahidan sun hada da yara kanana 66 da mata 39.

A ranar 10 ga watan Mayu Isra'ila ta fara kai hare-hare Zirin Gaza, kuma ta dakatar da hakan bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Hamas a ranar 21 ga Mayu.


News Source:   ()