Adadin mutanen da suka mutu a cikin ambaliyar ruwa a Beljiyom ya ƙaru

Adadin mutanen da suka mutu a cikin ambaliyar ruwa a Beljiyom ya ƙaru

Yayin da ake kokarin jinyar mutanen da suka samu raunuka a bala'in ambaliyar ruwan da ya afku a Beljiyom, an bayar da rahoton cewa adadin wadanda suka mutu ya karu zuwa 31 sannan kuma wadanda suka bace ya karu zuwa 163.

Ana ci gaba da aiyukan ceto wanda aka fara jiya tare da rage ruwan koguna.

An kuma ci gaba da aiyukan tsaftace wurare da gyara abubuwan da suka lallace, yayin da aka tantance cewa mutane 31 ne suka rasa rayukansu kuma ana neman mutane 163 da suka bace.

Firaminista Alexander de Croo ya fadi jiya cewa barnar da aka samu a duk fadin kasar tana da yawa kuma zai nemi tallafi daga Asusun Hadin Kan Tarayyar Turai.

A jihohin da ambaliyar ta shafa, gidaje dubu 37 har yanzu ba su da wutar lantarki.

Gwamnatin Beljiyom za ta aiyana zaman makoki a kasar a ranar 20 ga watan Yuli sannan ta soke bukin samun ‘yancin kan kasar da aka shirya gudanarwa a ranar 21 ga watan Yuli.

Mamakon ruwan saman ya shafi yankunan Liege, Verviers, Spa, Namur da Limburg da ke gabashin kasar.


News Source:   ()