Sanarwar tace adadin mutanen ya kai dubu 40 da guda 5, idan aka hada da wasu mutane 40 da ta kashe jiya, cikin su harda wata uwa da jariranta 'yan biyu da ta haifa a jiya.
Sanarwar ta kungiyar Hamas ta ce mutanen da suka jikkata sun kai dubu 92 da 401 sakamakon yakin da aka kwashe watanni 10 ana tafkawa, tun bayan harin da mayakan Hamas suka kai wa Israila a ranar 7 ga watan Oktobar bara. Hararen Isra'ilar sun hada da makarantu da asibitoci da sansanonin 'yan gudun hijira.
A yau ne ake komawa tattaunawar zaman lafiyar da Amurka ke jagoranci tare da kasashen Masar da Qatar wanda kungiyar Hamas tace ba zata halarta kai tsaye ba.
Yadda asibitin Al Shifa ya koma REUTERS - Dawoud Abu AlkasShugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ayau ya shaidawa taron majalisar dokokin kasar Turkiya na musamman cewar zai koma Gaza tare da sauran shugabannin kungiyar.
Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da Israilar ke ci gaba da kai munanan hare haren sama wadanda ke matukar illa ga mazauna yankin.
Daga cikin kasashen da suka gabatar da bukatar gaggauta kawo karshen yakin a gaza harda kasashen Birtaniya da Jamus da kuma Faransa, wadanda suka gabatar da sanarwar hadin gwuiwa a ranar litinin da ta gabata.
Majalisar dinkin duniya ta gudanar da tarurruka da dama domin nuna muhimmancin tsagaita wutar amma Isra'ila ta sa kafa ta shure bukatar, inda ta sha alwashin ci gaba da hare haren har zuwa lokacin da za ta murkushe mayakan Hamas baki daya.
Isra'ilar ta gindaya sharuddan tsagaita wutar da take bukata cikin su harda sakin daukacin 'yan kasar ta da aka yi garkuwa da su ba tare da gindaya sharidodi ba.
Rahotanni sun ce ya zuwa wannan lokaci hare haren na ta sun yi sanadiyar lalata birnin na Gaza baya ga kashe wadannan mutane sama da dubu 40.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI