Adadin mutanen da aka kashe a Myammar ya karu

Adadin mutanen da aka kashe a Myammar ya karu

Mutane 714 ne suka rasa rayukansu samakon afkawa masu zanga-zangar adawa da juyin mulki da kama shugabannin siyasa da sojojin Myammar suka yi.

Rahoton da Kungiyar Taimakawa Fursunonin Siyasa ta fitar ya ce, a awanni 24 da suka gabata an sake kashe mutane 4 wanda ya kawo adadin wadanda aka kashe a rikicin zuwa mutane 714.

Haka zalika ya zuwa yanzu an kama mutane dubu 3 da 054 a fadin kasar.

Rahoton ya bayyana an bayar da umarnin kama wasu mutanen 717.

A gefe guda, tashar talabijin ta MRTV ta bayyana cewa, an yankewa wasu masu fafutuka 6 da ke adawa da juyin mulki hukuncin kisa.

A ranar 9 ga Afrilu kotun soji ta fara yanke hukuncin kisa ga mutane a kasar inda aka kashe wasu mutane 19 da aka kama.

An bayyana cewa, mtanen 19 da aka kashe na da hannu a kisan wani jami'in soja a garin Yangon a ranar 27 ga Maris.


News Source:   ()